NDLEA ta kama wani da koken kunshe a cikin kwaroron roba a Fatakwal

0
105

Hukumar da ke yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce ta kama wani dan kasar Suriname dauke da hodar ibilis har kilo 9.9 da aka kunshe ta cikin kwaroron roba.

A wata sanarwa da ta fitar, NDLEA ta ce ta kama mutumin ne a filin jirgin sama na Fatakwal da ke jihar Ribas a kudu maso kudancin kasar.

“Jami’an NDLEA sun kama wani dan yankin Kudancin Amurka mai shekara 34 dauke da kunshin hodar ibilis 117 da aka dura a kwalaben turare aka kuma kunshe cikin wani katon kwaroron roba, ya shiga da su Nijeriya,” in ji sanarwar.

Kamen na NDLEA yana cikin manya da hukumar ta yi a jihohi biyar a cikin makon da ya gabata.

Ta kara da cewa mutumin ya sanar da hukumomin cewa ya bar kasarsa ne ranar 2 ga watan Afrilu ya tafi birnin Soa Paulo na Brazil.

“Daga can kuma sai ya tafi Nijeriya inda ya isa ranar 7 ga watan Afrilu don neman mahaifinsa dan Nijeriyar da ya dade da bata, kamar yadda ya yi ikirari,” in ji NDLEA.

Can a tashar jiragen ruwa ta Tincan da ke gabar teku a birnin Ikko na kudu maso yammacin kasar, NDLEA ta yi wani wawan kamun ne na kunshi 110 na hodar ibilis da aka boye a wata kwantenar kaya da ta isa Nijeriya daga birnin Montreal na Kanada.

Kazalika an kama wasu mutum biyu a hanyar Zariya zuwa Kano da wiwi mai nauyin kilogiram 148, sannan an yi kamen kilogiram 418 dauke a cikin wata mota kirar Sienna da za a kai wata matattarar masu aikata miyagun laifuka a Lagos.

A jihar Imo da ke kudu maso gabashi ma an kama wasu mutane dauke da maganin tari na kodin da wiwi mai yawa za su yi safarar su zuwa wani yankin kasar.

Wadannan kame na zuwa ne mako guda bayan da hukumar NDLEA ta kulla yarjejeniya da hukumar hana fasa kwauri ta kasar, Custom, kan yadda za su yi aiki tare don dakile safarar miyagun kwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here