Ramadan: Yobe ta ware Naira miliyan 103 don ciyarwa da wa’azi

0
154

Gwamnatin Yobe ta ware Naira miliyan 103 domin ciyar da marasa galihu da kuma kula da malamai masu wa’azi a lokacin azumin watan Ramadan na bana a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a garin Damaturu na jihar Yobe, Kwamishinan Harkokin addini, Alhaji Mala Musty, ya ce Gwamna Buni ya amince da kashe “Naira miliyan 73 wajen sayen raguna da kayan dafa abinci a cibiyoyin ciyar da abinci 67 da aka samar a jihar tun farkon azumin zuwa yanzu har kaiwa ga karshensa in sha’a Allah.”

An kuma ware Naira miliyan 30 domin biyan alawus ga malamai masu wa’azi da a lokacin azumin na bana a jihar.

“Mun shirya sanya jami’anmu su zagaya don duba duk wuraren da ake ciyar da abincin, don ba za mu iya barin haka ba don mutane su je su yi duk abin da suka ga dama,” in ji kwamishinan addinin.

Ya ce tun kafin zuwan Gwamna Buni al’adar gwamnatin Jihar Yobe ce ciyar da mabukata a watan Ramadan da sunan “Iftar”.

Kwamishinan addinin ya bayyana cewa gwamnati ta ware buhunan shinkafa 1,050 domin ciyarwan har zuwa karshen watan Ramadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here