Wani bene mai hawa hudu dauke da mutane ya rufta a Marseille

0
111

Rugujewar wani bene mai hawa hudu da ke tsakiyar birnin Marseille, birni na biyu na Faransa, ya yi sanadiyar raunata akalla mutane biyar, inda ake kyautata zaton akwai wasu mutane karkashin baraguzan ginin da ya rufta  in ji magajin garin birnin.

A nasa bangaren, Christophe Mirmand, shugaban yankin da ke kudancin Faransa ya shaidawa AFP cewa, “Akwai kwakkwaran zato cewa fashewar gas ta haifar da rugujewar jirgin, amma dole ne mu yi taka tsantsan game da musabbabin faruwar lamarin a wannan mataki”

A lokacin fashewar, da misalin karfe 12:40 na safe , “komai ya girgiza, mun ga mutane suna gudu kuma hayaki ya taso ko’ina, ginin ya fadi a kan titi.

“Dole ne mu shirya don samun wadanda abin ya shafa a cikin wannan mummunan bala’i,” in ji Benoît Payan, magajin garin Marseille. Tuni mutane biyar daga gine-ginen da ke makwabtaka da su suka jikkata.

Ayyukan ceto na da sarkakiya ganin “wuta  da ke ci a cikin baraguzan ginnin” wanda “ya hana aikewa da karnuka da tawaga don neman wadanda abin ya shafa da za su kasance karkashin baraguzan ginin”, in ji magajin garin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here