Wasu jerin ‘yan kulob daya da suka bai wa hammata iska

0
409

Ranar Laraba Sadio Mane da Leroy Sane suka yi fada a dakin hutun ‘yan wasa, bayan tashi daga Champions League, kamar yadda wasu jaridu suka wallafa.

Manchester City ce ta doke Bayern Munich 3-0 a wasan farko zagayen quarter finals a gasar zakarun Turai a Etihad.

Kamar yadda Bild da Sky da wasu jaridun Jamus suka wallafa, ‘yan wasan biyu sun bai wa hammata iska, bayan tashi daga karawar har sai da aka shiga tsakaninsu.

Bild cewa ta yi Mane ya naushi Sane tsohon dan kwallon City a fuska, har lebensa ya dan tsage.

Ba wannan shine karon farko da aka yi fada tsakanin ‘yan kungiya daya ba, ko dai a wajen atisaye har a filin wasa ko bayan an kammala gasa.

Wasu lokutan sai ka tsaya ka yi tunani me zai sa ‘yan kungiya daya su yi fada a tsakaninsu har da dukan juna.

Bayern ta dakatar da Sadio Mane daga buga mata wasa ranar Asabar, ta kuma ce za ta hukunta shi.

Ga jerin wasu daga fada da aka yi tsakanin ‘yan kungiya daya:

Ibrahimovic da Onyewu

Zlatan Ibrahimovic ya yi kaurin suna wajen fada da abokan taka ledarsa, ya taba yi wa Rafael van der Vaart barazanar zai karya masa kafa a Ajax ya kuma naushi Jonathan Zebina a fuska a Juventus.

To sai dai wanda ya fi mune shine wanda ya yi a AC Milan, inda ya yi fada da Oguchi Onyewu, wanda ke taka leda aro a Newcastle United daga kungiyar Italiya.

Batty da Le Saux

Blackburn Rovers ta kasa taka rawar gani a Champions League, bayan lashe Premier League.

A lokacin ta ziyarci Spartak Moscow a wasa na biyar a cikin rukuni, bayan kasa yin nasara a fafatawar biyar.

A Rashan an ci Blackburn 3-0 a wasan ne David Batty da Graeme Le Saux suka dunga dukan juna da kyar aka raba su.

Drinkwater da Jota

Ba za ka taba cewa ‘yan wasan da suka yi zaman benci za su bai wa hammata iska ba, abin da ya faru tsakanin Drink Water da Jota kenan a wajen atisaye.

Kwana daya tsakani da Aston Villa ta ci Leicester City 4-0 – ‘yan wasan Leicester da ba su buga karawar ba na atisaye a Bodymoor Hearth – sai cece kuce ya barke tskanin Drinkwater da Jota, inda ‘yan wasan Ingila suka yi wa kansu gware, sai da aka shiga tsakaninsu

Tottenham ta yi nasara a kan Everton da cin 1-0 a Yulin 2020, amma batun da ya fi jan hankali bayan hutu shine rigima tsakanin Gugo Lloris da Son Heung-min.

Golan Tottenham ya tuhumi Son da kin dawowa ya tare kwallo – daga baya suka barke da kokawa har sai da Giovani Lo Celso da Harry Winks suka shiga tsakini, da aka tashi daga wasan sun rungumi juna.

Bayan tashi daga wasan koci, Jose Mourinho ya ce abin da ya faru abin ban sha’awa ne.

Mitrovic da Kamara

Aleksandar Mitrovic da Aboubakar Kamara sun dambata a tsakaninsu, bayan da Kamara ya karbe kwallo daga hannun dan Serbia suna Fulham ya buga fenariti a karawa da Huddersfield – akuma bi ci ba.

Adebayor da Bendtner

Emmanuel Adebayor shima daya daga ‘yan wasan da ke fada da abokan wasansa ne, sun bai wa hammata iska da Kolo Toure a Manchester City a lokacin atisaye a 2011.

Tun kan nan Adebayo ya yi fada da Nicklas Bendtner a Arsenal a 2008, wanda aka ce ya yi wa dan kasar Denmark gware a wasan da Tottenham ta ci 5-1 a League Cup wasan daf da karshe.

Robben da Ribery

An yi fada tsakanin Arjen Rubben da Frank Ribery a lokacin Champions League tsakanin Bayern Munich da Real Madrid.

‘Yan wasan biyu sun yi takaddama kan wanda zai yi bugun tazara – an yi zargin Ribery ya naushi Robben – amma Bayern ba ta ce komai kan lamarin.

Shearer da Gillespie

An yi wani kazamin rikici tsakanin Alan Shearer wanda ta kai sai da aka dangana da Keith Gillespie zuwa asibiti ‘yan wasan Newcastle United a 1997.

Lehmann da Amoroso

Jens Lehmann bai da hakuri ko kadan, ya kuma kalubalanci Marcio Amoroso, bayan da Schalke ta zura kwallo a kungiyarsu Borussia Dortmund a 2003.

An bai wa Lehman jan kati a karawar, wanda ya zama golan farko a Bundesliga mai wannan tarihin da aka kora karo na hudu – daga baya aka soke kwallon da cewar akwai satar gida – inda suka tashi canjaras.

Ljungberg da Mellberg

Mare-mare aka yi tsakanin Freddie Ljungberg da Olof Mellberg, wanda hakan ya ja hankalin manema labarai a lokacin da ake shirin zuwa gasar kofin duniya a 2002.

Ricksen da Radimov

Shi dama Fernando Ricksen mafadashi ne, wanda ya yi rigima da kyaftin, Vladislav wata daya da komarsa Zenit tun kan nan ya yi rigima da Malaga a lokacin atisayen tunkarar kakar tamaula.

Fadan da aka yi tsakanin ‘yan kulub daya a tarihi yana da yawa da aka yi a baya, za kuma a ci gaba da yi duk da matakan ladabtarwa da kungiyoyi ke dauka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here