Da dumi-dumi: INEC ta bayyana Alhassan Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben Doguwa da Tudun Wada

0
150

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa Alhasan Ado Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar tarayya da zai sake wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun wada.

Jami’in zaben, Farfesa Sani Ibrahim, wanda ya bayyana sakamakon zaben a zaben da aka kammala na mazabu takwas a karamar hukumar Tudunwada, ya ce Doguwa ya samu kuri’u 41,573.

Babban abokin hamayyarsa, Yushau Salisu na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 34,831, kamar yadda jaridar r Daily Trust ta rawaito.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a zaɓen da aka gudanar a Ranar 25 ga watan fabarairun shekara 2023, an bayyana Alhassan Ado a matsayin wanda ya lashe zaben, sai dai daga bisani hukumar zabe ta ce takurawa Baturen zaɓen aka yi ya bayyana sakamakon, bayan kuma zaɓen bai kammala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here