Masallacin Ƙudus na Musulman duniya ne – Mabiya Shi’a

0
100

A ranar Juma’a ne ’yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky, waɗanda aka fi sani da mabiya Shi’a a Nijeriya suka bi sahun ‘yan uwan su a duniya wajen gudanar da jerin-gwano don tunawa da masallacin Ƙudus. 

An gudanar da wannan jerin gwano a kusan duk manyan biranen ƙasar nan, wanda ya haɗa da Kaduna.

Ana yin jerin-gwanon duk shekara-shekara ne na goyon bayan Falasɗinawa da ake gudanarwa a ranar Juma’ar ƙarshe ta watan Ramadan don nuna goyon baya ga Falasɗinawa da adawa da Isra’ila da yahudawan sahyoniya.

An kuma gudanar da ranar Qudus a wasu ƙasashe da dama musamman a ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen Musulmi, inda ake gudanar da zanga-zangar nuna adawa da mamayar da Isra’ila ke yi a gabashin birnin Ƙudus. Ana gudanar da taruka a ƙasashe daban-daban na al’ummar Musulmi da ma waɗanda ba Musulmi ba a duniya.

A shekarar 1979 aka fara yin wannan jerin-gwano a ƙasar Iran.

A jawabin da wakilin mabiya Shi’a a Kaduna Kaduna ya yi, Sheikh Aliyu Tirmizi, ya ce, “mun fito ne domin nuna adawarmu ga gallaza wa al’ummar Falasɗinu da kuma mamayar da Isra’ila ke yi a birnin Ƙudus, wanda muka saba fitowa a duk ranar Juma’ar ƙarshe ta watan Ramadan.”

Sheikh ɗin ya kushe abubuwan da ke faruwa a ƙasar Falasɗinu, harda dawo da masallacin Al-Aqsa birnin Qudus da kuma cigaba da kashe Falasɗinawa da ƙasar Isra’ila ta ke yi.

Malamin ya ƙara da cewa, “muna fitowa ne cikin tsari, amma a wasu lokuta jami’an tsaro su kan far mana babu gaira, babu dalili, inda a bara sai da suka kashe mana mutane da dama. A bana ma sun far mana da hayaƙi mai sa hawaye tare da harba harsasai masu rai, inda suka harbi sama da mutum 20”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here