Rahotanni daga Jihar Neja a tarayyar Najeriya na cewa mutane akalla 50 ne suka rasa rayukan su a karamar hukumar Ibbi, sakamakon wata arangama tsakanin ‘yan sintiri da kuma ‘yan ta’adda da suka addabi wannan yanki.Â
Ana dai zargin wadannan ‘yan ta’adda sune suka kutsa kai kauyen, a makon jiya, inda suka hallaka mutane da dama, yayin da suka yi garkuwa da guda 12.
Bincike ya nua cewa ‘yan sintirin ne suka farwa ‘yan ta’addar a maboyar su, yayin da suka hallaka da dama daga cikin su, bayan sun lalata sansanonin su dake kewayen Wajen shakatawa na Kainji, yayin da suka shafe tsahon kwanaki 4 suna artabu da juna.
Yayin rikicin dai 9 cikin mutane 12n da ‘yan bindigar suka sace a makon jiya sun kubuta cikin su har da magatakardar babbar kotun shari’ar musulunci ta jihar da kuma mata guda 6.