Air Peace ya yi tayin kwaso ‘yan Najeriya da ke Sudan kyauta

0
56

Kamfanin sufurin jirgin saman Air Peace ya yi tayin bayar da gudumawar kwaso daliban Najeriya da suka makale a Sudan kyauta

Onyeama ya ce Najeriya ta shirya tsaf don fara kwaso al’ummar ta daga Sudan din.

Fiye da ‘yan Najeriya dubu biyar ne yanzu haka ke makale a Sudan, wadanda mafi yawan su mata ne musamman a birnin Khartoum, inda barin wuta ya fi muni, kuma kawo yanzu suna ta kiraye-kiraye ga gwamnati da ta kawo musu daukin gaggawa.

Wannnan dai ba shi ne karon farko da kamfanin Air Peace ke irin wannan aiki na kwaso ‘yan Najeriya a kasashen da suke fama da rikici ba, don kuwa ko a shekarar 2019 sai da ya kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a Africa ta Kudu bayan barkewar rikicin wariyar launin fata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here