Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 63, sun ceto mutum 150 da aka sace

0
126

Hedikwatar rundunar tsaro ta sojin Nijeriya ta bayyana cewa dakarunta sun yi nasarar halaka ‘yan ta’addar Boko Haram 63 tsakanin farkon watan Maris zuwa 15 ga watan Afrilu.

Baya ga kashe ‘yan ta’addan, sojojin sun kuma ceto sama da mutane 150 da aka sace a yayin gudanar da ayyuka daban-daban a wasu yankunan kasar nan.

Manjo Janar Musa Danmadani, daraktan yada labarai na tsaro ya shaida wa manema labarai a hedikwatar tsaro a ranar Alhamis, cewa sojojin da suke aikin sun kuma kwato kayayyaki da dama da suka hada da bindigogi 36 ak-47, AK-47, da sauran manyan makamai.

Sauran sun hada da kayan abinci, babura, abubuwan fashewa shanu daga hannun ‘yan ta’addar.

 

Ya kuma bayyana cewa sojojin sun kwato danyen mai na sata da kuma gas na mota wanda kudinsu ya kai naira miliyan N259m daga hannun tsagerun yankin Neja Delta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here