Gwamnatin Najeriya ta kara albashin ma’aikata da kaso 40 cikin 100

0
103

Karin albashin ya shafi ma’aikatan da ke karkashin tsarin biyan albashi na bai daya su dubu 144,766, yayin da kuma karin zai zarce har kan alawus-alawus dinsu.

Wannan na nufin sauran ma’aikatan gwamnatin tarayyar kasar da ke karkashin wasu tsare-tsare ba zasu mori wannan karin albashin ba.

An dai cire ma’aikatan lafiya da malaman jami’o’i daga tsarin karin albashin ne, kasancewar ba sa karkashin tsarin biyan ma’aikatan na bai daya.

Sauran wadanda ba za su mori sabon albashin sun hada da jami’an jinya, ma’aikatan jami’o’i, jami’an ‘yan sanda da kuma sojoji.

A wata wasika da hukumar kula da biyan albashin Najeriya karkashin jagorancin Ekpo Nta ta fitar, ta ce iyakacin ma’aikata 144,766 ne za su mori wannan cigaba.

Tuni dai kungiyar manyan malaman jami’a ta ASUU a kasar ta yi wa wannan sabon tsari fuskar shanu, tana mai cewa babu dalilin da zai sanya a cire tadaga cikin ma’aikatan da za a yi wa karin albashin, duk kuwa da an yi musu karin a baya-bayan nan.

Shugaban kungiyar na kasa Farfesa Emmanuel Osedeke ya zargi gwamnatin da yunkurin haifar da matsala, yana mai cewa kungiyar za ta nazarci wannan batu, kuma za ta sanar da matakin da za ta dauka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here