Babu hanyar tserewa daga yankin da ake rikici a Sudan – Hausawan Sudan

0
133

Mazauna birnin Khartoum a Sudan na ci gaba da tserewa daga ƙasar bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin da ke yaƙi da juna a ƙasar.

Yaƙin da ake yi a Sudan ya jefa jama’a cikin halin tsaka mai wuya – babu abinci kuma babu ruwan sha sannan farashin kayayyaki ya tashi sosai.

BBC ta samu zantawa da daya daga cikin Hausawan Sudan da suke zaune a birnin na Khartoum – cibiyar rikicin.

Mudassir Annur Zakariya, wani Hakimi a Kudancin Khartoum ya bayyana irin halin fargaba da tashin hankalin da suke ciki sanadin rikicin da ake yi a ƙasar ta Sudan.

Harsashi idan aka sake shi, ko ina zai iya faɗawa saboda farar hula suna gamuwa da haɗari da yawa a wannan yaƙi da ake yi.” in ji Mudassir Annur Zakariya.

Mudassir Annur Zakariya ya ce yaƙin ya shafe su sosai kasancewar suna zaune ne a birnin na Khartoum sannan yaƙin da ake yi a Khartoum ake yinsa.

Ya kuma ce yaƙin da ake yi ya sa al’ummar ƙasar yin tsokaci kan halin da ake ciki, “Wasu na cewa bai dace a ce an yi yaƙin nan a cikin mutane cikin al’ummar farar hula kuma a tsakiyar gari,”

“Kuma su sun san mutane ne manya ne da makamai – wannan ɓangaren da makamai, wannan ma haka, ya kamata a ce an zauna an san me ya kamata a yi an sasanta.” in ji Hakimin.

Mudassir ya ce duk da cewa mutane da dama suna barin ƙasar domin neman tsira, su har yanzu suna cikin ƙasar saboda “idan ka gudu ma, ba maganar tsira bane.”

Ya ce inda suke, rikicin bai ƙazanta ba shi yasa suke ci gaba da zama a ƙasar duk da halin da ake ciki.

“Abin ba shi da tsanani ne a ɓangarenmu nan na Kudancin Khartoum- wajensu Kalakla da Mayo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here