Ya akai Ministocin Nijar suka fi shugaban kasar samun kuɗi?

0
88

Al’ummar Jamhuriyar Nijar na ci gaba da muhawara cikin mamaki game da irin tarin kadarorin da wasu ministocin ƙasar suka mallaka.

Rahoton kotu na shekara-shekara ya nuna cewa wasu ministoci dai sun mallaki dukiyar da ta kama daga mafi yawa saifa biliyan bakwai (N7bn) zuwa mafi ƙaranci saifa miliyan ɗari (N100m).

Kotun dai ta bayyana rahoton da shugaban ƙasa da ministocin gwamnatinsa da ‘yan majalisar dokoki da shugabanin hukumomi da sauransu suka ayyana dukiyar da suka mallaka a 2022.

‘Yan Nijar da dama sun cika da mamaki ganin yadda za a ce wani ministan ƙasar ba tare da wasu harkokin kasuwanci da suka bayyana a zahiri ba, zai mallaki irin wannan maƙudan kuɗi cikin ƙanƙanin lokaci.

Mafi jan hankali a cikin rahoton 2022 na dukiyar da jami’an gwamnati suka mallaka kamar yadda aka wallafa shi ne yadda ministoci da dama suka fi Shugaba Mohammed Bazoum mallakar dukiya.

Kotun dai ita ce ke sa ido a kan kashe kuɗaɗen gwamnati a Jamhuriyar Nijar.

Doka ce ta tilasta wa duk wani jami’in gwamnati da muƙaminsa ya kai girman ya bayyana dukiyar da yake da ita, kafin hawansa muƙamin.

Kuma dole jami’in gwamnati ya riƙa sabunta bayani duk shekara a kan dukiyar, matuƙar yana kan muƙami, abin da ke bai wa al’ummar Nijar damar sanin irin abubuwan da ke ƙaruwa a kan dukiyar jami’an gwamnati.

A cewar Micheal Zodi shugaban wata ƙungiyar sa-ido a Nijar siyasar ce ta zama tamkar wani kasuwanci a ƙasar, inda ya yi zargin cewa ‘yan siyasar na azurta kansu da kuɗaɗen yi wa talakawa aiki.

Kiran a yi bincike – Masu gwagwarmaya

Micheal Zodi ya ce “Kwalliya ta biya kuɗin sabulu, daga cikin siyasa ne suka samu waɗannan kuɗaɗen tun da su ba ‘yan kasuwa ba ne. Kuma ba su gaji kuɗin daga ko’ina ba.

Tsirarun mutane ne masu kuɗi, amma talakawa suna fama da wahalhalu na rashin kuɗi da rashin abinci, in ji ɗan gwagwarmayar.

 Ita ma ƙungiyar FSCN ta yi zargin cewa wasu jami’an gwamnati da karkatar da dukiyar ƙasa, abin da ya sanya su tara irin waɗannan maƙudan kuɗi.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Idi Abdu ya ce bai yi mamaki ba ganin yadda Nijar ke ci gaba da talaucewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here