Gwamnatin Lagos ta sayo motocin bas masu aiki da lantarki

0
32

Gwamnatin Jihar Lagos da ke kudancin Nijeriya ta ce ta sayo sabbin motoci masu amfani da lantarki don yin aiki da su a matsayin motocin haya.

Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.

Ya ce an sayo bas-bas din ne da zummar saukaka sufuri da rage tasirin sauyin yanayi a Lagos, birni mafi girma a Afirka da ke da mutane fiye da miliyan 15.

Wannan ne karon farko da hukumomi a Nijeriya suka sanar da sayo irin wadannan motoci domin yin sufuri.

Mr Sanwo-Olu ya ce matakin zai tabbatar da ”tsaftace tsarin sufuri” a birnin.

”Sabbin motocinmu masu aiki da lantarki za su inganta sufuri da rage gurbatar muhalli. Hakan na nufin mazauna birnin Lagos za su yi daina aiki da fetur su soma amfani da makamashi mai tsafta,” a cewar gwamnan a wata sanarwa da ya fitar.

Kawo yanzu ba a san adadin motocin bas din da gwamnatin ta saya ba amma Gwamna Sanwo-Olu ya ce za a karo motoci masu yawa da ke aiki da lantarki don inganta sufuri a birnin.

Ya kara da cewa nan da watanni masu zuwa za a soma amfani da motocin a “matakin gwaji.”

A cewarsa hakan zai bai wa gwamnati damar ”tattara isassun bayanai game da aiki da makamashi maras gurbata muhalli” da kuma kwatanta shi da yadda ake aiki da fetur da zummar inganta tsarin sufuri.

‘Yan kasar sun yi maraba da wannan mataki ko da yake wasu sun nuna dari-dari game da dorewarsa ganin yadda shirye-shirye da dama da gwamnatoci ke bijirowa da su suke lalacewa.

Nijeriya ta yi kaurin suna wurin dauke wutar lantarki don haka mutane ke ganin zai yi wahala matakin ya dore.

Wasu kuma sun bayyana cewa cunkoson ababen hawar da ake fama da shi a Legas zai zama kalubale ga wannan shiri.

Sai dai gwamnati ta ce za ta samar da “tashoshin da za a rika yin cajin motoci masu aiki da lantarkin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here