Kwamitin Majalisar Dattawa da ke kula da harkokin waje na Najeriya ya musanta zargin da wani dan majalisar Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba ya yina almundahana a harkar aikin Hajji.
Shugaban kwamitin Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa ne ya musanta zargin a wata hira da BBC.
Shugaban kwamitin ya ce ya tun da farko ya shirya sauraron jin ra`ayin jama`a kan hukumar alhazan kasar da kyakkyawar niyya ta neman shawarwarin da za su taimaka wajen inganta ayyukanta.
A wata hira da yayi da BBC a karshen mako dan Majalisar Dattijai mai wakiltar Sokoto ta Kudu Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba ya yi zargin cewa wani bincike da ya gudanar ya gano ana almundahana a harkar aikin Hajji.
Ya ce “binciken ya gano ana sama da fadi da kudaden mahajjata, otel da ya kamata a kama na kwana arba’in sai a kama na tsawon kwana casa’in sauran kwanakin kuma sai a sanya Larabawa a dakunan bayan alhazai sun tafi, sai a raba kudin tsakanin masu otel da kuma shugaban Hukumar Alhazai na wancan lokacin inda otel zai dauki kashi 25 shi kuma shugaba ya dauki kashi 75” a cewar Sanata Dan Baba.
Amma a martanin kwamitin da ke kula da harkokin waje na majalisar ta dattijai shugaban kwamitin Sanata Bulkachuwa ya ce ciniki akeyi a kan abunda ya shafi kudin hayar gidaje da jirage da tantuna har a samu daidaituwa don haka babu ta inda mutum zai sa aikin Hajji ya yi tsada.
Har’ilayau Bulkachuwa ya ce kwamitin ya fuskanci jinkiri wajen samun kudin aiki sannan lokaci ya kure amma duk da haka an kira mutane kuma an ji. ra’ayinsu kan batun.
“Shi sha’anin kudin Hajji ba Hukumar Alhazai ce kadai za ta ce mun kayyade kaza ba, ita ma Saudiyya tana da doka da ka’idojinta” in ji shi.
Ya kara da cewa babu yaudara ko kuma jan kafa a cikin aikin da kwamitin ya yi sannan babu wani nufi na shiririntar da wani kudiri da Sanata Ibrahim Abdullahi wanda ya yi zargin ya gabatar.
A shekarar 2023 dai Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya ta kayyade kudin aikin Hajjin a kan Naira miliyan 2.8 ga kowane maniyyaci.
An shafe shekaru da dama ana kwan-gaba-kwan-baya kan batun yin gyara ga dokar a gaban majalisar dokokin ta Najeriya.