A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na Twitter, NAFDAC ta ce ba ta yi wa taliyar Indomie ta ‘Special Chicken Flavour’ rajista ba.
“Akwai bukatar a san cewa taliya na daga cikin jerin abubuwan da gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta haramta shiga da su, hakan na nufin ba a yarda a rika shigar da ita Nijeriya,” a cewar sanarwar.
Tun a karshen makon jiya ne rahotanni suka fara watsuwa cewa hukumomin lafiya na kasashen Malaysia da Taiwan sun gano sinadarin da ke jawo cutar kansa a cikin taliyar Indomie mai dandanon.
Wannan lamari ya sa wasu kasashen duniya musamman inda taliyar wacce asalinta daga kasar Indonesiya ne, ta fi karbuwa suka fara daukar matakai.