Najeriya za ta soma gwaji kan ingancin taliyar Indomie

0
81

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta ce ranar Talatar nan za ta soma gwaji kan ingancin taliyar Indomie a fadin kasar.

Ta bayyana haka ne sakamakon rahotannin da ke cewa taliyar na dauke da sinadarin ethylene oxide wanda ke haddasa cutar daji.

A wata sanarwa da ta fitar, Shugabar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce: “Sashen da ke kula da ingancin abinci na hukumarmu zai fara gwaji kan taliyar Indomie a ranar 2 ga watan Mayun nan.

“Abin da ake son dubawa shi ne sinadarin ethylene oxide. Tuni an bai wa daraktan kula da dakunan gwajin abinci wannan aikin. Yana aiki kan fayyace bayanan da aka tattara,” in ji ta.

Farfesa Mojisola ta ci gaba da cewa “Dama dai an san cewa an dade da hana shigar da Indomie kasar tsawon shekaru da suka wuce. Tana daya daga cikin jerin abincin da gwamnati ta haramta shiga da su. An haramta ta a Nijeriya kuma NAFDAC ba ta yi mata rijista ba.

Shugabar ta NAFDAC ta ce abin da suke yi a yanzu shi ne sake yin taka-tsantsan don tabbatar da cewa ba a shigar da taliyar cikin kasar ta haramtacciyar hanya ba, “idan kuma har an yi hakan, to jami’anmu da ke sa ido za su gano ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here