Home Labarai Ranar Ma’aikata: Masu zanga-zanga sun raunata ‘yan sanda 108 a Faransa

Ranar Ma’aikata: Masu zanga-zanga sun raunata ‘yan sanda 108 a Faransa

0
63

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewar, masu zanga-zangar a birnin Paris sun jefi ‘yan sanda tare da fasa gilasan wuraren kasuwanci irin su bankuna da sauran su, lamarin da ya sanya jami’an tsaro yin amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi wajen tarwatsa su.

Kungiyoyin kwadago sun bukaci jama’ar kasar su fito zanga-zangar ta ranar ma’aikata, don kara sukar tsarin Macron, wanda ke neman kare sauye-sauyen da ya samar.

Ma’aikatar Kula da Harkokin Cikin Gida ta kasar ta ce kimanin mutane dubu 782 ne suka gudanar da zanga-zanga a fadin kasar, ciki kuwa har da mutane dubu dari da 12 da suka yi ta su a birnin Paris, duk da cewa kungiyar kwadago ta kasar ta ce adadin ya zarce haka domin a nata alkaluman, mutane miliyan biyu da dubu dari uku ne suka fito don yin zanga-zangar a fadin kasar, ciki kuwa har da mutane dubu dari biyar da 50 da suka gudanar da ta su a babban birnin kasar.

A watan da ya gabata ne Macron ya rattaba hannu kan dokar da ta kara shekarun yin ritaya daga aiki daga 62 zuwa 64.

Tun a tsakiyar watan Janairu ne dai ake ta gudanar da yajin aiki da kuma zanga-zanga a kasar akan sauyin da Macron ya yi wa tsarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp