‘Yan Real Madrid da suka je Sociedad buga La Liga

0
98

Real Sociedad ta karbi bakuncin Real Madrid, domin buga wasan mako na 33 a La Liga ranar Talata a Estadio Anoeta.

Ranar 29 ga watan Janairun 2023, Real Madrid da Real Sociedad suka tashi 0-0 a wasan farko a kakar bana.

Real Madrid tana mataki na biyu a kan teburi La Liga da maki 68, ita kuwa Sociedad mai maki 58 tana ta hudu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis Lopez.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. da kuma Rudiger.

Masu buga tsakiya: Kroos, Valverde, Tchouameni, D. Ceballos, Dotor, Arribas da kuma Nico Paz.

Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Rodrygo, Mariano da kuma Alvaro.

Da zarar Real ta kammala karawa da Sociedad za ta buga wasan karshe a Copa del Rey da Osasuna ranar 6 ga watan Mayu.

Daga nan ne Real za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan daf da karshe a Champions League a Santiago Bernabeu ranar Talata 9 ga watan Mayu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here