‘Yancin ‘yan jarida ne ‘yancin duniya

0
49
Antonio Guterres ya jajantawa ‘yan jarida da kafafen yada labarai na duniya yana mai cewa duk ‘yancin al’umma ya dogara ga aikin ‘yan jarida

Ana kai hare-hare kan yancin ‘yan jarida a kowane lungu da sako na duniya, in ji babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya.

Yana mai yin tir da yadda ake kai wa ‘yan jarida hari da yada labaran karya. Da yake jawabi gabanin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya da za a yi a gobe Laraba, sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya jajantawa ‘yan jarida da kafafen yada labarai na duniya. Yana mai cewa “Dukkan ‘yancinmu ya dogara ne ga ‘yancin ‘yan jarida,”

Guttres ya cigaba da cewa  “tushen dimokuradiyya da adalci” da kuma “rayuwar kare hakkin bil’adama.” su nake nufi. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya kara da cewa, “Amma a kowane lungu na duniya ana kai wa ‘yancin ‘yan jarida hari.”.

Dama dai ana bikin yancin ‘yan jarida a fadin duniya ranar uku ga watan maris na ko wace shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here