David Beckham na tseren dauko Messi da Saudiya

0
109

Kulob din Inter Miami na tsohon dan wasan Manchester United da Ingila David Beckham ma na hamayya da Al-Hilal na Saudiyya wajen zawarcin Lionnel Messi. (Guardian)

Real Madrid na tattaunawa kan dauko dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, sai dai kungiyar ta Jamus ta ce har yanzu ba ta samu tayi daga kungiyar ta Spaniya ba. (Sky Germany)

Sheikh Jassim ya yi watsi da shirin siyan dan wasan gaba na Brazil Neymar Jn, mai shekara 31, idan batun komawarsa Manchester United ya tabbata – maimakon haka zai fara zawarcin ‘yan wasan irinsu Kylian Mbappe na Faransa da PSG, mai shekara 24, da Kingsley Coman na Bayern Munich, 26, da Eduardo Camavinga na Real Madrid, mai shekara 20. (Bild’s Christian Falk)

Dan wasan tsakiya na West Ham da Ingila Declan Rice, mai shekara 24, da dan wasan gaban Bayer Leverkusen dan kasar Faransa Moussa Diaby, mai shekara 23, da kuma Wilfried Zaha, mai shekara 30, na Ivory Coast da kuma Marc Guehi na Ingila, mai shekara 22, suna cikin mutum shida da kocin Arsenal Mikel Arteta ke fatan sayen su a bazara.(Mail)

Har ila yau, Chelsea na sha’awar Zaha, wanda sabon kocin ta mai jiran gado Mauricio Pochettino ya yi kokarin dauko shi tun lokacin da yake horas wa Tottenham.(Mail)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here