Majalisar Dinkin Duniya ta amince da sakacinta a rikicin Sudan

0
93

Mista Antonio Guterres wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Nairobi babban birnin kasar Kenya inda yake ziyara kan rikicin na Sudan, yace an yi wa Majalisar Dinkin Duniya ba zata game da rikicin, saboda abin da suka sani shine yadda wasu kasashen duniya suka wuce gaba a kokarin ganin an mika mulki ga farar hula.

Guterres yace, a yayin da suke jiran ganin kokarin mika mulki ga farar hula, sai kwasam suka ji fada ya barke a Sudan, kuma hakan na fitar da gazawarsu a bayyane.

Gwagwarmayar neman mulki

Jami’in yace al’ummar Sudan basu cancancin wannan hali da aka shiga ba, saboda dama can sun dade da tagayyara kawai saboda sun kai na janar-janr din biyu dake gwagwarmayar neman mulki.

Tun a ranar 15 ga watan Afrilu kazamin fada ya barke a manyan biranen Sudan ciki harda Khartoum fadar gwamnatin kasar, tsakanin shugaban kasar Abdel Fattah al-Burhan, wanda ke jagorantar sojoji gwamnati, da mataimakinsa da ya koma abokin gaba Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar dakarun sakai na RSF.

An kashe sama da mutun 550

Akalla mutane 550 ne aka kashe sannan wasu 4,926 suka jikkata, a cewar alkaluman ma’aikatar lafiya na baya-bayan nan.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekarar 2019, masu shiga tsakani na kasa da kasa suka yi ta kokarin sassanta farar hula da sojoji domin zama teburin tattaunawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here