An cafke matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Kano

0
57
Kano

Matashin nan da ya caka wa mahaifiyarsa wuka ya kashe ta a Jihar Kano ya shiga hannun ’yan sanda.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito kakakin ya ruwaito kakakin ’yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, yana cewa, “Matashin ya amsa abin da ake zargin ya aikata da kuma yin fataucin miyagun kwayoyi.”

Matashin mai shekara 22 ya kashe mahaifiyar tasa mai shekaru 50 ne ta hanyar sossoka mata wuka a sassan jikinta, saboda wata sabani da suka samu.

Daga nan ya cika wandonsa da iska, kafin makwabta su shiga su same ta kwance cikin jini, su garzaya da ita asibiti.

Aminiya ta ruwaito cewa matashin, wanda ake wa lakabi da Kwarangwal, ya yi wannan aika-aika ne a unguwar Rimin Kebe da ke Karamar Hukumar Nassarwa ta Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa matashin, wanda ake wa lakabi da Kwarangwal, ya yi wannan aika-aika ne a unguwar Rimin Kebe da ke Karamar Hukumar Nassarwa ta Jihar Kano.

NAN ya ruwaito kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, yana cewa rundunar ta yi nasarar cafke matashin a wata maboyar bata-gari da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta jihar.

Tun a ranar Alhamis Kiyawa ya ce sun fara farautar matashin bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here