Kasuwar Alaba da ke Legas ta yi gobara

0
37

Babbar kasuwar Alaba da ke yankin Ojo a Jihar Legas ta kama da gobara a ranar Juma’a.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Legas ta ce gobarar ta fara ne daga bacocin da ke kasuwar, ta ci gaba da ci.

Kakakin hukumar Margaret Adeseye ta bayyana cewa gobarar ta fara ne da tsakar dare sakamakon matsalar wutar lantarki.

Ta ce jami’an hukumar na kokarin shawo kan wutar, amm ta nuna damuwa cewa wasu fusatattun mutane sun hana motocin kashe gobara da suka taso daga wasu yanki domin kawo dauki a shawo kan wutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here