Osimhen ya taimakawa Napoli lashe kofin Seria A na farko cikin shekaru 33

0
62

Victor Osimhen ya kafa tarihi a daren Alhamis inda ya taimakawa Napoli wajen samun damar lashe kofin Seria A na Italiya karon farko cikin shekaru 33.

Dan wasan gaban na Najeriya ya zura kwallo mai mahimmanci a mintuna na 52 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci wajen farke kwallon da Sandi Lovric ya ci wa Udinesse daga fara wasa.

Canjaras dama Napoli ke bukata domin lashe gasar Seria A ta bana, kuma ta yi nasara aka tashi kunnen doki 1-1.

Kwallo daya mai ban haushi da Osimhen ya zurawa Udine shine na 22 a wasanni 28 da ya buga a wanna kaka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here