‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda uku a kudancin Anambra

0
53

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar,Tochukwu Ikenga da ya tabbatar da faruwar lamarin da yammacin Alhamís, ya kuma ce ‘yan bindigan sun budawa jami’an wuta ne a yayin da suke kan aiki, abinda ya yi sanadiyar mutuwar 3 daga cikin su.

Rahotanni suka ce mazauna kusa da wurin sun ranci na kare domin kaucewa harbe harben da ‘yan bindigan suka yi ta yi babu kakkautawa.

Anambara na daga cikin jihohin kudancin Najeriya dake fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga masu dauke da makamai wadanda ake zargi mayakan haramtaccen kungiyar IPOB masu neman kafa kasar Biafra ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here