Adadin shi ne kusan duk matasa biyar a cikin maza 100, kuma ɗaya cikin ‘yan mata 100, in ji hukumar ƙididdiga a ƙasar.
Duk da yake, ba lallai ne hakan ya janyo alamomi ko matsaloli ba, amma lamari ne da ke ƙara tarawa zuciya da jijiyoyin jini gajiya.
Hawan jini ne ke haddasa kusan rabin matsalolin bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki a Birtaniya
Mutum na iya kamuwa da cutar hawan jini a kowanne zango na rayuwarsa, shi ya sa ma likitoci suka ce ya kamata manya su riƙa zuwa gwajin jini a kai a kai, su kuma ɗauki matakan kare illarsa ta dogon lokaci.
Chris Shine, daga hukumar ƙididdigar ya shaida wa BBC cewa sun yi nazari domin gano rukunin da suka fi fuskantar hatsarin kamuwa da ɓoyayyiyar cutar hawan jini a jiki.
“Mun ga cewa akwai adadin matasa da mutane masu lafiya da ba a duba su ba. Ta yiwu wannan rukunin ba su san suna ɗauke da matsalar ba saboda ba za su iya samun kulawa ba idan suna da lafiya,” in ji shi.
“Wannan sakamako zai samar da ƙarin bayani ga cibiyoyin kula da lafiya da waɗanda ke neman inganta sakamakon, abin da ya zama daga cikin sanannun abubuwan da ke janyo mutuwar wuri, musamman kasancewar mun san cewa gano cutar hawan jini da wuri kan taimaka wajen kula da matsalar a tsakanin kowane rukunin shekaru.”
Kusan kashi ɗaya bisa uku na manya a Birtaniya na da hawan jini amma galibi ba su san suna da matsalar ba, in ji ƙwararru.
Kasancewar nauyin mutum ya wuce ƙima da cin abinci mars gina jiki da kasala da shan barasa da kuma shan taba duka na janyo matsalar hawan jini.
A cewar hukumar ƙididdigar, samari ne suka fi yiwuwar ba za a iya gano su ba – kashi 66 cikin 100 na maza da kashi 26 cikin 100 na mata ƴan shekara 16 zuwa 24 da kashi 55 cikin 100 na maza da kashi 44 cikin 100 na mata ƴan shekara 25 zuwa 34, idan aka kwatanta da kashi 17 cikin 100 na maza da kashi 21 bisa 100 na mata masu shekara 75 zuwa sama.
Ƙididdigar ta fito daga nazarin lafiya na Ingila wanda ya bi gida-gida domin yi wa mutane 20,000 gwajin jini ciki har da matasa 1,500 – da wani ma’aikacin jinya ya yi a lokuta daban-daban domin gano matsakaicin bayani kan yanayin jinin mutanen.
Ya bayyana cewa:
Kashi 4 cikin 100 (kimanin 110,000) da kashi 7 cikin 100 na maza (kimanin 210,000) ƴan shekara 16 zuwa 24 a Ingila suna da hawan jini.
Daga cikinsu, kashi 26 cikin 100 na mata (kusan 30,000) da kashi 66 cikin 100 na maza (kusan 140,000) ba a duba su ba.
Dakta Pauline Swift, daga cibiyar agaji ta charity Blood Pressure UK, ta ce yayin da ba a iya kaucewa wasu abubuwa da ke tunzura cutar kamar tsufa da asali, wasu kuma mutane na iya magance su.
“A shekarun baya-bayan nan, mun ga ƙaruwar matasa masu hawan jini, galibi sakamakon rashin abinci mai gina jiki da yawan cin gishiri da rashin motsa jiki abin da ke janyo mutum ya ƙara nauyi,” in ji ta.
“Idan ka soma yin ƴan sauye-sauye ga tsarin rayuwarka a lokacin da kake matashi, kamar rage yawan cin gishiri da shan kayan marmari da cin ganye da motsa jiki domin inganta lafiyarka, toh ka fi yiwuwar zama cikin ƙoshin lafiya tare da kare kamuwa da shanyewar ɓarin jiki da cututtukan zuciya da cutar ƙoda.
“Hawan jini na kashe dubban mutane kowace shekara a Birtaniya kuma galibi abu ne da ake iya magancewa.
“Ya kamata kowa ya ɗauki lafiyarsa da muhimmanci ta hanyar gwajin jininsa ko dai a gida ko a kantin sayar da magunguna ko a wajen ma’aikatan jinya. Wannan na iya kare rayuwarka.”
Farfesa Bryan Williams, Shugaban Ƙungiyar masu fama da hawan jini ta duniya kuma ƙwararre a asibitin koyarwa na Jami’ar kwalejin London ya ce: “Bana tunanin mutane sun fahimci haɗarin zama da hawan jini ba tare da magani ba.
“An ƙiyasta cewa hawan jini na janyo mace-mace miliyan 10 duk shekara a sassan duniya. Hakan na nufin ƙarin mace-mace a duniya duk shekara a kan adadin mace-macen da aka samu a duniya sakamakon annobar korona cikin shekara uku.
“Labari mai faranta rai shi ne da zarar an gano mutum na ɗauke da hawan jini, ga akasarin mutane, ya fi sauƙi wajen kula da shi musamman idan aka gano da wuri.
“Idan ina da saƙo, shi ne, ku riƙa auna jininku, kada kuma ku yi burus idan jinin ya hau.”
Jini ya kasance tsakanin 90 bisa 60mmHg da 120 bisa 80mmHg, shi ne tabbacin lafiya.