An nada sabon sarkin Ingila karon farko tun bayan shekaru 70

0
65

An gudanar da gagarumin bikin nadin Sarki Charles na III a wannan Asabar, inda Arcbishop na Canterbury ya sanya masa kambin sarautar Ingila domin maye gadon mulki na marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu, bikin da shi ne irinsa na farko cikin shekaru 70.

Mahalartar bikin sun bige da sowa a yayin sanya masa kambin na zinari wanda aka samar a karni na 17

Wannan biki shi ne irinsa na farko tun bayan wanda aka yi a shekarar 1937 lokacin da aka nada mahaifiyarsa.

Wannan gagarumin bikin ya samu gayyatar shugabannin kasashen duniya da kuma manya manyan ‘yan kasuwa da fitattun mutane sama da 2,300 wadanda yanzu haka ke birnin London domin halartar bikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here