An ci gaba da luguden wuta a Sudan gabanin tattaunawar tsagaita wuta a Saudiyya

0
111

Luguden wuta ta sama ya wujijjiga babban birni Sudan, Khartoum a ranar Asabar, a yayin da rikicin daa ake yi ya shiga mako na 4, sa’o’i gabanin tattaunawar tsagaita wuta a Saudiyya tsakanin bangarorin da ke rikici da juna.

Daruruwan mutane ne suka mutu tun bayan da wannan  rikici ya tashi a ranar 15 ga watan Afrilu a tsakaani n rundunar sojin  kasar da daakarun kai daukin gaggaawa na kasar a karkashin  jagorancin mataimakin shugaban kasar, Mohamed Hamdan Daglo.

A wata sanarwar hadin gwiwa, Amurka da Saudiyya sun ce rundunar sojin Sudan da bangaren RSF za su gudanar da tattaunawa a birnin Jeddah, suna mai bayyana shi a matsayin tattaunawar sharer fagen kulla yarjejeniyar tsagaita wuta.

Tun da aka fara wanna rikici jiragen yaki ne aka gani suna ruwan bama-bamai a wurare dabam –dabam na birnin Khartoum, a yayin da mayakan Janar-Janar din soji biyu da ke rikici da juna suna ta bai wa hammata iska a birnin mai yawan al’umma miliyan 5.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here