Real Madrid ta lashe Copa Del Rey karo na 20 a tarihi

0
66
Soccer Football - Copa del Rey - Final - Real Madrid v Osasuna - Estadio de La Cartuja, Seville, Spain - May 7, 2023 Real Madrid's Karim Benzema celebrates with the trophy and teammates after winning the Copa del Rey REUTERS/Jon Nazca

Real Madrid ta lashe kofin gasar Copa del Rey bayan ta lallasa Osasuna a wasan karshe da suka fafata a ranar Asabar.

Kusan shekaru goma rabon da Real Madrid ta lashe kofin gasar na Copa del Rey, inda a yanzu ta lashe 20 jimilla a tarihi.

Real Madrid ta samu nasara wasan karshe na Copa del Rey bayan ta doke Osasuna da ci 2-1, ta hannun kwallaye biyu da dan wasanta na Brazil, Rodrygo ya jefa a minti na biyu da kuma na 70 da soma wasan.

Sai dai Osasuna ta mayar da martani bayan kwallon farko da aka jefa ta, inda ta farke a minti na 58 ta hannun Lucas Torro.

Aminiya ta ruwaito cewa an fafata wasan ne a filin wasa na La Cartuja mai daukar ’yan kallo 57,619 kuma filin wasa na biyar mafi girfa a duk ilahirin Sifaniya.

Madrid ta lashe wasan na karshe duk da cewa a yanzu tana taga-taga a gasar La Liga.

Wasan dai shi ne karon farko da Osasuna ta yi harin lashe wani babban kofi.

Sai dai duk da goyon bayan da Osasuna suka rika samu daga magoya bayansu 25,000 don ganin sun dauki wani babban Kofi a karon farko a tarihinsu na shekara 103, ba su yi nasara ba.

Gabanin wannan nasara ta yanzu, sau 19 Madrid tana lashe kofin na Copa del Rey, inda ta lashe karo na karshe a shekarar 2014.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here