ISWAP ta kashe manoma 3, ta sace 11 a Borno

0
88

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargi mayakan kungiyar nan mai ikirarin jihadi a Yammacin Afirka (ISWAP), sun kashe manoma uku tare da sace wasu 11 a kauyen Bulayobe da ke kusa da garin Banki a Jihar Borno.

Majiyar ta bayyana cewar, manoman sun yi tafiyar kilomita 10 a wajen Banki don share gonaki a shirye-shiryen tunkarar damina, inda ake sa ran fara saukar ruwan sama na shekara-shekara a cikin kwanaki nan.

“Kamar yadda rahoton da ya fito daga Zagazola Makama, kwararren mai fashin baki kan tayar da kayar baya da sha’ani tsaro a Tafkin Chadi,ya ce ’yan kungiyar ISWAP wanda duka-duka yawan su bai wuce takwas ba dauke da makamai ne suka shiga cikin gonaki a kan babura hudu sannan suka yi awon gaba da manoma 14 da ke aikin share gonakinsu,” in ji Usman Hamza, shugaban ’yan sa-kai da ke yaki da ’yan ta’addan tare da sojoji.

“Daga baya, wata tawagar bincike ta gano gawarwakin manoma uku tare da aka harbe yayin da sauran manoman 11 har yanzu ba a gano inda suke ba,” in ji Hamza.

Wani mazaunin Banki, Kabir Abdu ya bayyana cewa abokinsa na cikin wadanda aka kashe sannan kuma akwai wani dan uwansa da ke cikin wadanda aka nema aka rasa.

A makon jiya ne dai wasu masu yankan katako 15 suka yi layar zana a garin Gamboru da ke yankin da mayakan Boko Haram ke kai hare-hare.

Washegarin ranar ce aka gano gawarwaki hudu a cikin daji yayin da har kawo yanzu ake laluben inda sauran 11 suka shiga, in ji Umar Kachalla, wani dan gwagwarmayar a Gamboru.

“Mun gano gawarwakin hudu amma mun gaza gano sauran 11 bayan bincike mai zurfi,” in ji Kachalla.

“Mun zargin mayakan Boko Haram na rike da su,” in ji shi.

Boko Haram da takwararta ISWAP wadanda kuma suke hamayya da juna, sun saba kai hare-hare kan masu yankan katako, makiyaya, manoma, masunta da masu tara karafa.

Kungiyoyin ta’addan na zargin mazaunan da yi wa sojoji leken asiri tare da kwarmata musu bayanai a kan duk wani shige da fice nasu.

Wadannan hare-haren na nuni da irin yadda fararen hula ke fuskantar matsalolin  a yankunan karkara, fiye da shekaru 14 da fara ta da kayar baya a yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.

Duk da haka hukumomin yankin sun rufe sansanoni da dama na wadanda rikicin ya raba da muhallansu tare da mayar da mutane gida, suna masu cewa ya kamata su koma gona don sake gina rayuwarsu.

Matsalar tsaro dai babbar barazana ce kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a Afirka, lamarin da ake fuskanta yayin da ake shirin rantsar da sabon shugaban kasa a cikin wannan wata bayan zaben da aka gudanar a watan Fabrairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here