Matashin da ke burin ƙera wa sojojin Najeriya jiragen yaƙi

0
87

Wani matashi mai fasahar ƙere-ƙere a Najeriya ya ce ya fara tunanin ƙera wa sojojin Najeriya jirgin sama na yaƙi maras matuƙi ne a lokacin da aka sace ɗaliban sakandiren Kankara su fiye da 300.

Matashin mai suna Ashiru A. Ashiru ya ce ya yi wannan tunani ne domin jami’an tsaron su samu sauƙi a yaƙin da suke yi da ta’addancin a faɗin ƙasar.

Ashiru wanda ke da digiri a ilimin Sifa wato Physics daga jami’ar Alqalam da ke Katsina a arewacin Najeriya ya ce ya yi wannan aiki ne, domin nuna wa duniya irin baiwa da fasahar da Allah Ya yi wa Najeriya.

Matashin ya ce tun yana jami’a yake da sha’awar ƙere-ƙere, inda shi da abokan karatunsa suka ƙera wani ƙaramin jirgin sama mai saukar ungulu.

”A lokacin da aka sace ɗaliban Sakandiren Kankara sai na fara tunanin ƙera wani jirgi maras matuƙi da zai iya gano inda waɗannan ɗaliban suke”, in ji matashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here