PSG na zawarcin Mourinho, Messi da Al Hilal sun kasa cimma matsaya

0
84

Mai bayar da shawara kan harkokin kwallon kafa na Paris St-Germain Luis Campos ya yi magana da wakilin Jose Mourinho a kan zama kociyan kungiyar ta Faransa a bazaran nan. (RMC Sport).

Lionel Messi, wanda kwantiraginsa da PSG zai kare a bazara, bai cimma yarjejeniyar komawa Al Hilal ta Saudi yya ba, kuma ba a sa ran tauraron na Argentina zai yanke shawara kan makomarsa har sai zuwa karshen kakar wasa ta Faransa ranar 3 ga watan Yuni. (Mundo Deportivo)

Chelsea na duba yuwuwar sayar da dan gabanta na Amurka Christian Pulisic, a karshen kakar nan, kuma za ta iya hadawa da shi ta sayar wa Napoli domin zakarun nta Italiya su sayar mata da Victor Osimhen, na Najeriya. (Mail)

Barcelona ta yi wa Raphinha, wanda Newcastle United da Chelsea ke so, farashin yuro miliyan 80, kungiyoyin Premier na sha’awar ganin sun dawo da tsohon dan Leeds din kuma dan Brazil gasar ta Ingila. (Sport)

Bayer Leverkusen ta sake bayyana aniyarta ta sayen dan wasan tsakiya na Arsenal Granit Xhaka, bayan da kungiyar ta Jamus ta yi kokarin sayen dan wasan na Switzerland a bazarar da ta wuce. (Mirror)

West Ham ba ta son a hada da wani dan wasa a cinikin Declan Rice, maimakon haka tana son duk kungiyar da za ta sayi dan wasan tsakiyar na Ingila ta biya ta fam miliyan 100 kawai kafin ta bar shi ya tafi a bazara mai zuwa. (Football Insider)

To amma kuma dan wasan tsakiya na Marseille Matteo Guendouzi, na Faransa zabi ne da zai iya maye gurbin Rice a West Ham din kasancewar daman tana ganin tsohon dan Arsenal din a matsayin wanda zai iya cike gurbin kyaftin din nata. (Athletic – subscription required)

Dan gaban Faransa Randal Kolo Muani zai kai yuro miliyan 90 ga duk kungiyar da ke bukatar sayensa in ji shugaban Eintracht Frankfurt Axel Hellmann. (90 Min)

Matashin dan wasan Crystal Palace Michael Olise, mai shekara 21, na daukar hankalin Paris St-Germain, wadda ke son taya dan tawagar Faransa ta ‘yan kasa da shekara 21 a bazara. (Mail)

Bayanai na nuna cewa Aston Villa da Leeds United da kuma West Ham na sha’awar dan gaban Lyon Moussa Dembele, na Faransa, wanda ya taba taka leda a Fulham da Celtic. (Birmingham Mail)

Dan wasan tsakiya na Brazil Arthur Melo na son samun damar yin wasan da zai yi ban-kwana da abokan wasansa da sauran ma’aikan kungiyar Liverpool da kuma magoya baya wadanda ya ce sun kyautata masa, kasancewar bai samu damar taka leda sosai a kungiyar ta Anfield ba tun da ta karbo shi aro daga Juventus tsawon kaka daya. (Goal)

Crystal Palace da Fulham da West Ham da kuma wasu na Faransa da Sifaniya na daga kungiyoyin da ke sha’awar dan wasan tsakiya na Clombia da Bournemouth Jefferson Lerma, wanda kwantioraginsa zai kare a bazaran nan. (Teamtalk)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here