Tafiyar Busquets dama ce ga Barcelona ta dawo da Messi – Tebas

0
66

Tebas ya kare kalaman nasa da cewa sai Barcelona ta rabu da wani dan wasa mai jan kudi ne za ta iya sake dakko Messi da ta ke kwadayin dawo da shi kungiyar.

A jiya ne dai Busquets wanda shi ne Kyaftin din Barcelona a yanzu ya tabbatar da jita-jitar raba gari da kungiyar tasa tun ta yarinta ko da ya ke bai sanar da inda zai koma ba, amma ya nanata cewa sam baya son rabuwa da kungiyar ta Catalonia.

A bangare guda Messi wanda bayanai ke cewa PSG b ata da Shirin tsawaita kwantiraginsa, jita-jita na alakanta shi da komawa Saudiya da taka leda don bin sahun babban abokin dabinsa wato Cristiano Ronaldo da ya koma Al Nassr a watan Janairu, inda wata majiya mai kusanci da shi Leo ke cewa Saudiyan ta yi masa tayin da bazai iya kawar da kai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here