Makiyaya sun kashe zakuna shida da suka addabi ƙauyensu

0
108

Makiyaya sun kashe wasu zakuna shida a gundumar Kajiado na ƙasar Kenya, bayan da zakunan suka kwashe tsawon daren Asabar suna far wa mazauna ƙauyen Nashipa.

Rahotonni sun ce zakuna 11 da suka tsere daga gandun dajin ‘Amboseli National park’, suka afka wa ƙauyen tare da addabar al’ummar ƙauyen na tsawon dare guda.

Zakunan sun yi ta far wa gidajen mutane inda suka kashe tumaki 11 tare da kare guda, a wani lamari da wani mazaunin ƙauyen ya bayyana da ‘daren subhana’.

“Yunkurin da masu tumakin suka yi na ƙubutar da su ya ci-tura, tumaki ne da suka tsallake-rijiya-da-baya daga masifar fari da ƙasarmu ke fuskanta, amma sai ga shi sun ƙare a matsayin kalacin zakuna,” in ji wani mazaunin ƙauyen.

A ranar Asabar da safe ne gwamman mazauna ƙauyen suka ɗauke da kwari da baka da wasu makaman suka ƙaddamar da farautar zakunan tare da kashe shida daga cikinsu.

Jami’an kula da gandun dajin ƙasar da jagororin kauyen da sauran masu ruwa da tsaki sun gudanar da ganawar gaggawa kan lamarin da maraicen ranar Asabar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here