- Recep Tayyip Erdogan: Shi ne shugaban ƙasar na yanzu, ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Turkiyya a shekarar 2014, bayan ya kwashe shekara 11 a matsayin firaministan ƙasar tun daga shekarar 2003, lokacin da jam’iyyarsa ta AKP ta samu rinjaye a zaɓen majalisar dokokin ƙasar.
- Kemal Kilicdaroglu: Dan takarar ƙawancen jam’iyyun adawa shida da ke da manyan ‘yan takarkaru a muƙaman majalisar dokokin ƙasar. Tun shekarar 2010 ne Mista Kilicdaroglu ke jagorantar haɗakar jam’iyyun adawa a ƙasar.
- Sinan Ogan: Dan gwagwarmayar kishin ƙasa, damarsa ta yin nasara a zaɓen ba ta da yawa.