Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram da dama a yankin Tafkin Chadi

0
119

Dakarun rundunar hadin-gwiwa ta Multinational Joint Task Force da ke aiki a yankin Tafkin Chadi sun kashe mayakan Boko Haram sannan suka kwato makamai masu yawa.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ta MNJTF Kanal Kamarudeen Adegoke ya fitar ranar Lahadi, ta ce dakarun sun samu wannan nasara ne karkashin shirin nan na Operation Harbin Kunama.

Rundunar ta bayyana cewa bayan ta dakile harin da kungiyar Boko Haram da ISWAP suka kai a yankin Arege, rundunar ta yi kokarin kai samame a yankin a ranar 11 ga watan Mayu.

Sanarwar ta ce dakarun sun kashe ‘yan Boko Haram da dama, ko da yake ba ta bayyana adadinsu ba.

An kwato abubuwa da dama ciki har da bindigar harbo jirgi da kuma a-kori-kurar da ake girke bindiga, kamar yadda sanarwar ta ce.

‘Yan Boko Haram 974 sun mika wuya a Nijeriya

Haka kuma sanarwar ta ce rundunar ta kai wani samame a yankin Ferondiya da ke yankin Tafkin Chadi inda ta tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda.

Rundunar ta MNJTF ta ce ta kwato a-kori-kurar da ake girke bindiga da kuma bindigar harbo jirgin sama biyu da makamin RPG da AK 47 biyu da bam din RPG da motoci uku kirar Toyota da ake girke bindiga.

Sauran abubuwan da aka gano sun hada da harsasai 387 nau’in 12.7mm sai harsasai 440 nau’in 7.62mm da 54mm sai kuma harsasai 364 nau’in 7.62mm da 50mm. Rundunar ta Multinational Joint Task Force ta kunshi dakaru daga Nijeriya da Niger da Kamaru da Benin da Chadi inda kuma hedikwatar rundunar take a Chadi.

Abin da ta sa a gaba a halin yanzu shi ne yaki da mayakan Boko Haram da Iswap wadanda suka yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma raba miliyoyi da muhallansu a Yammacin Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here