Bani da wani gida a kasar waje -Buhari

0
128

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, bai mallaki wani gida a kasar waje ba.

Buhari ya sanar da hakan ne, a lokacin da ya karbi wasikun kama aiki na babban kwamishina da aka turo Nijeriya daga Landan, Richard Hugh Montgomery da takwaransa ba Sri-Lanka Velupillai Kananathan.

Shugaban wanda ya karbi wasikun nasu a yau Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce, ya kuma sanar da hakan ga Sarki Charles na III a lokacin wata ganawa da suka yi bayan da Charles ya tambaye shi, cewa ko yana da gida a Landan.

A cewarsa, “A ganawar da na yi da Sarki Charles na III, ya yi min tambayoyi masu ma’ana, inda daga ciki ya tambaye ni, ko ina da gida a Landan, ni kuma na mayar masa da amsa cewa, ban da gida ko da kafa daya, a wajen Nijeriya.

”Ya ci gaba da cewa, musayar al’adu ta hanyar ilimin zamani da samar da horo a tsakanin Nijeriya da Landan, abu ne da aka shafe shekaru da dama ana yi, inda ya kara da cewa, ya samu horon zamowa jami’in soja Mons ne, a makarantar Aldershot da ke Landan daga 1962 zuwa 1963, inda ya ce, ya kuma yi kwas din jami’in zama bakaniken sufuri a makarantar soji ta koyon kanikancin sufuri ta Borden, da ke a Landan a 1964.

Buhari ya shaida wa Montgomery cewa, fahimtar banbance -banbancen al’adu da kuma girmama al’adun ne, babban ginshikin da ya sa Landan ta samu nasara, inda ya sanar da cewa, jakadun baya, sun sun kafa kyakyawar danganta da Sultan na Sokoto da kuma Sarkin Kano, Shehun Borno, da Sarkin Ilorin.

Buhari ya shaida wa Montgomery cewa, ako da yaushe, ya ci gaba da riko da ingancin jakadanci, kamar yadda jakadun baya, da aka turo Nijeriya suka yi, mussaman wajen girmama al’adun Nijeriya.

Shugaban ya bayyana cewa, Nijeriya za ta kara karfafa huldar jakadanci da ke a tsakanin Landan da kuma Sri Lanka, musamman wajen girmama al’adun kasahen biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here