Firaministan Japan Fumio Kishida na karbar bakuncin shugabannin daga wasu kasashe shida masu karfin tattalin arziki, a guda daga cikin biranen kasar da ya taba fuskantar harin makaman nukiliya, kuma a yanzu cike yake da abubuwan tunawa.
Shugabanni da suka hada da shugaban Amurka Joe Biden za su yi kokari na tsawon kwanaki uku don samar da hadin kai a kan Rasha da China, inda sau dama maslahar kawance kasashen ba sa samar da mafita.
Shirin warware rikicin diflomasiyya da ya dabaibaye shugaba Biden a yankin Asiya ya ci karo da cikas tun kafin ya bar kasar Amurka, sakamakon takaddamar kasafin kudi na cikin gida da ya tilasta masa soke tsayawa a Papua New Guinea da Australia.
Yunkurin mamayar da Rasha ta yi na watanni 15 a Ukraine, shi ne kan gaba wajen tattaunawa a kai a taron kolin G7 a ranar Juma’a, bayan wani sabon hari ta sama da aka kai a Kyiv da kuma Bakhmut da sauran garuruwan Ukraine.
Amurka da kawayenta sun tura makami zuwa Ukraine domin dakile ci gaban da Rasha ta samu, amma har yanzu ba a kai ga dakatar da kai hare-hare da sojojin Kyiv suka dade suna fafutuka a kai ba.
Ana sa ran shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky zai yi jawabi ga shugabannin kungiyar ta yanar gizo