Gwamnatin Nijeriya ta fitar da jadawalin mako daya na bikin mika wa zababben shugaban kasar Bola Tinubu mulki ranar 29 ga watan Mayu don zama shugaban kasar na 16.
Sakataren Gwamnatin kasar kuma shugaban kwamitin mika mulki, Boss Mustapha, ya bayyana ranar Alhamis cewa za a yi shagali na mako daya zuwa 29 ga watan Mayu ranar da Shugaba Muhammadu Buhari zai mika mulki ga shugaba mai jiran gado Bola Tinubu.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, babban birnin kasar Boss Mustapha ya ce ranar Talata, 23 ga watan Mayu 23, za a yi liyafa ta girmamawa ta soji ga shugaba mai barin gado, Muhammadu Buhari.
Ranar 24 ga watan Mayu 24 (Laraba), za a yi taron bankwana na Majalisar Ministoci a Fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Kazalika ranar 25 ga watan Mayu (Alhamis), za a karrama Tinubu da babban lambar yabo ta GCFR da ake bai wa shugabannin kasa kadai. Har wa yau a ranar, Buhari zai karbi lambar yabo ta GCON da ake bai wa tsofaffin shugabannin kasar. A yayin bikin, Buhari zai mika takardun mika mulki ga Tinubu.
26 ga watan Mayu (Juma’a), za a gabatar da lacca da sallar Juma’a a babban masallacin kasa da ke Abuja tsakanin karfe 10 na safe zuwa 1:30 na rana.
A ranar 27 ga watan Mayu (Asabar), Tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, zai ba da lacca kan “hanyoyin zurfafa dimokuradiyya don cudanya da ci gaba”.
A ranar 28 ga watan Mayu (Lahadi), za a gudanar da taro na mabiya addinin Kirista a cibiyar kiristoci ta kasa da ke Abuja. A yammacin ranar, Shugaba Buhari zai karbi bakuncin baki da suka zo don a yi liyafar cin abincin dare a dakin taro na fadar gwamnati.
A ranar 29 ga Mayu (Litinin), Tinubu zai yi rantsuwar kama aiki a dandalin Eagle Square da ke Abuja da misalin karfe 10 na safe agogon kasar. Haka kuma za a gudanar da faretin kaddamarwa.
Sannan kuma za a gudanar da liyafar cin abincin rana bayan rantsar da shi a dakin taro na Banquet House da misalin karfe 1:30 na rana. Tinubu ne ya shirya liyafar, kuma ana sa ran shugabannin kasashen da aka gayyato da shugabannin gwamnati da manyan baki ne kawai za su halarci taron.
Kwamitin mika mulki ya ce an gayyaci shugabannin kasashe da na gwamnati da dama, kuma akasarinsu sun ba da tabbacin cewa za su halarci bikin mika mulkin Nijeriya ga Bola Tinubu.
Shugaban kwamitin, Boss Mustapha, ya ce ba zai iya bayyana adadin ko sunayen shugabannin da aka gayyata ba saboda “sha’ani na tsaro”.
Tinubu, wanda ya yi takara a jam’iyyar APC mai rike da mulki, ya samu kuri’u miliyan 8.8 kuma an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Nijeriya da aka gudanar a watan Fabrairun 2023.
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya zo na biyu da kuri’u miliyan 7, yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya zo na uku da kuri’u miliyan 6.1.
Atiku da Obi sun yi wasti da sakamakon zaben, kuma sun shigar da kara a gaban kotun zabe, suna kalubalantar nasarar da Tinubu ya samu.