Shugaba Buhari ya nada sabuwar babbar akantar Najeriya

0
229

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin babbar Akanta Janar ta tarayya.

Hakan na kunshe ne a wata takardar da shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esin, ta fitar, inda ta ce nadin nata ya fara aiki ne a ranar 18 ga watan Mayun 2023.

Har zuwa lokacin da aka nada ta, ta kasance Daraktar Kudi a ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Madein ta karbi mukamin ne daga hannun tsohon Akanta Janar na kasar, Ahmed Idris, wanda shugaba Muhammadu Buhari ya kora, kuma a halin yanzu yake fuskantar tuhuma daga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, kan badakalar cin hanci da bai gaza naira biliyan 100 ba.

Idris wanda aka nada akanta Janar a ranar 25 ga watan Yuni 2015, ya karbi mulki daga hannun Jonah Ogunniyi Otunla wanda shi ma shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kora bisa zargin karkatar da naira biliyan 2.5bn na kudaden hukumomin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here