Ba mu karɓi kuɗi ba kafin amincewa da buƙatar Buhari ta ciyo bashi – Yan majalisar wakilai

0
108

Yan Majalisar Wakilan Najeriya sun musanta zargin karɓar kuɗi dala miliyan 15 daga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kafin su amince da buƙatar sauya fasalin bashin naira tiriliyan 22 da ta karɓa daga Babban Bankin Najeriya (CBN).

Majalisar ta bayyana zargin da “maras tushe wanda kuma ba shi da makama” cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Benjamin Kalu, ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce sai da suka tattaunawa da ɓangaren zartarwa da kuma tsettsefe buƙatar kafin su amince.

“A matsayinmu na zaɓaɓɓun wakilai, matakai da kuma ayyukan da muke gudanarwa don al’umma ne.

“Idan ba a manta ba, Majalisa ta dakatar da buƙatar na wani lokaci don saboda shawarar da wasu kwamatoci suka bayar ta gudanar da cikakken nazari game da aikin tallafa wa al’umma da gwamnatin ta ce za ta yi da kuɗin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here