Wasu ‘yan siyasa na shirin guduwa kafin 29 ga watan Mayu – EFCC

0
53

Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce wasu ‘yan siyasa da take zargi da rashawa na ƙoƙarin ficewa daga ƙasar kafin su sauka daga mulki ranar 29 ga watan Mayu.

EFCC ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani ga Gwamnan Zamfara Bello Matawalle game da zargin da ya yi wa shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa cewa ya nemi rashawar dala miliyan biyu a hannunsa – kwatankwacin naira miliyan 922.

“Idan har Matawalle da gaske yake, ya kamata ya daina ɓaɓatu ya gabatar da hujja ƙarara kan zargin da yake yi,” in ji wata sanarwa da EFCC ta wallafa ranar Juma’a.

Ta ƙara da cewa: “Kazalika, hukumar na ankarar da al’umma cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ake zargi da cin hanci da rashawa da ke shirin ficewa daga Najeriya kafin ranar 29 ga watan Mayu.”

EFCC ta ce Gwamna Matawalle ya fara gabatar da zarge-zargen ne bayan ta ƙaddamar da bincike kan zargin almundahanar naira biliyan 70 a kansa na wasu ayyukan da ta ce an bayar amma ‘yan kwangilar ba su yi ba.

Bello Matawalle na jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar na cikin gwamnonin da za su sauka daga mulki a ranar 29 ga Mayu bayan ya sha kaye a hannun Dauda Lawal na PDP a zaɓen watan Maris da ya gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here