Nau’ukan abinci da za su iya taimaka wa ma’aurata samun haihuwa

0
76

Idan ka ziyarci kowanne zaure na tattaunawa a shafukan sada zumunta, abu guda da ake yawaita tafka muhawara a kai babu mamaki ba zai wuce batun nau’in abinci da za a iya ci domin kara damammaki daukar ciki ba.

Baya ga tarin magunguna masu ɗauke da sinadaran da ke taimakawa wajen saurin ɗaukan ciki, akwai kuma wasu jeren abinci da ya kamata a ce suna taimakawa wajen cimma burin samun juna-biyu cikin koshin lafiya da inganci.

Duk da tarin yanayi na tallata wasu magunguna ko hanyoyin taimakawa mace ta yi ciki a cikin gaggawa, mene ne gaskiya kan amfani ko yanayin cimaka wajen inganta damar samun ciki ga mata da inganta maniyyin maza, da kuma taimakawa rayuwar ɗan-tayi?

Da fari, idan aka zo kan batun inganta yanayin ɗaukar ciki da lafiyar ɗan-tayi, akwai wasu sinadarai da babu shaka za su iya taimakawa – kamar sinadarin folic acid.

Shan sinadarai kafin ciki da kuma lokacin da mace ta tabbatar tana da juna-biyu, ya tabbatar da nuna cewa yana kare jarirai daga samun nakasu, a kwakwalwa da wasu sassa na jiki.

Irin waɗannan nakasu a watannin farko na ciki ake gamuwa da su, a lokuta da dama tun kafin mace ta ankara cewa tana ɗauke da juna-biyu.

Cibiyar taƙaita da hana yaɗuwar cututtuka ta Amurka ta shawarci duk mace da ta kai shekarun haihuwa ta rinƙa shan sinadarin folic acid miligram 400 a kullum.

Akwai nau’ikan cimaka irinsu hatsi da ke ɗauke da sinadarin folic acid, da suke taimakawa sosai wajen bada kariya, saboda akasari ana ɗaukan ciki ba tare da an shirya ba.

An kiyasta cewa, a 2019, taron wayar da kawuna ya taimaka wajen kare kashi 22 cikin dari na matsalolin da rashin shan sinadarin folic acid ke haddasawa a faɗin duniya.

Folic acid na da karin amfani sosai a jikin dan adam: idan mace mai kokarin samun ciki ta na shan sa sosai, yana taimakawa damar daukan ciki, koda yake akwai bukatar sake gwaje-gwaje domin tabbatar da hakan.

To ina labarin sauran cimaka ko magunguna da suka kunshi sinadarai masu kara lafiyar jiki? Shin akwai wani abu da za a iya kira ‘abincin daukan ciki’ wanda zai inganta damar samun juna-biyu?

Wani bincike ya gano cewa cin nama ga maza na illa a kokarin haihuwa ta hanyar dashan dantayi a mahaifa wato IVF

Binciken da aka gudanar kan ma’aurata da ke shirin samun ciki ta hanyar dashan ɗan tayi a mahaifa wato IVF ya gano cewa cin nama ga maza, musamman wasu nau’ikan nama na haifar da matsala.

Karin haske kan wannan batu shi ne, yana taka rawa wajen asasa wasu matsalolin rashin samun ciki.

A Amurka, bayan shafe shekara guda ana jima’i ba tare da kariya ba, kashi 15 cikin 100 na ma’aurata sun kasa samun juna-biyu. Akwai dalilai da dama.

Daga ɓangaren macen, mai yiwuwa mahaifa ta kasa samar da lafiyayyun kwayayyen halitta ko kuma ya zamana kwayayyen ne ba su iya fitowa daga mabubbugarsu zuwa farfajiyar mahaifa (zuwa wurin kwanciyar jariri) -Misali saboda toshewar hanyar da suke biyowa ta cikinsa.

Ko da kuwa kwan ya yi nasarar fitowa, yana iya kauce hanya ko kuma ya kasa zama a cikin mahaifa.

A bangaren maza, maniyyi mai cikakken lafiya na da muhimmanci. Wannan ya kunshi kaurinsa, da yanayin yauƙi da kuma fitarsa da ma yawansa.

Akwai abubuwa da dama da ke barazana ko shafar lafiyar maniyyi mai inganci, ciki harda matsaloli masu alaƙa da muhalli kamar gurbatar yanayi.

A wasu lokuta ko da kuwa an gudanar da gwaji, matsalar rashin haihuwa ba lallai ya iya fitowa karara ba: kashi 15 cikin 100 na matsalolin ba a iya fahimtarsu ba.

Ko bayan samun ciki, nau’in cimakan uba na iya tasiri ga jaririn da ke ciki.

Wani bincike da Jami’ar Queensland ta Australia ta gudanar ya nuna cewa abubuwan da iyaye maza ke ci na tasiri sosai ga lafiyar ɗan-tayi.

Tawagar masu binciken sun nazarci yanayin cimakan ma’aurata 200 da ke goyon-ciki, a asibitin Mater da ke Brisbane.

Binciken ya gano cewa abincin da maza ke ciki ya yi tasiri sosai fiye da na uwa, wanda hakan ya yi tasiri kan jaririnta.

Sauran binciken ya nuna cewa nauyin jikin uba shi ma na tasiri sosai musamman kan nauyin jaririn da za a haifa.

A galibin lokuta ba a mayar da hankali kan lafiyar uba da yanayin cimakarsa domin iya bai wa mace ciki, amma gaskiya abu ne mai muhimmanci, a cewar Shelly Wilkinson, kwararriya kan abinci mai gina jiki a Jami’ar Queensland.

Masu bincike a Jami’ar Havard sun nazarci yanayin cimakan tawagar mata 18, 555 a tsawon shekara takwas, da ke kokarin daukan ciki da wadanda ke dauke da ciki.

Sun rinƙa cin sinadarin protein da ake samu daga tsirai, maimakon na dabobbi kamar cin jan nama, wanda aka gano sun fi samun kariya da kashi 50 cikin 100.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here