Buhari ya umarci shugabannin hukumar haɓaka arewa-maso-gabas da su kama aiki

0
94

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci membobin sabuwar hukumar gudanarwa ta Hukumar Haɓaka Arewa-maso-gabas (NEDC) da su kama aikin riƙon ƙwarya ba tare da ɓata lokaci ba don kada a bar wajen babu shugabanni.

 

Shugabannin za su yi aiki ne kafin su samu tabbacin naɗin su daga Majalisar Dattawa kamar yadda doka ta tanada.

Wata sanarwa ga manema labarai da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Dakta Nasir Sani-Gwarzo, ya rattaba wa hannu ta ce an yanke wannan shawarar ne don kada a bar wajen babu shugabanni.

Haka kuma shugaban ƙasa ya amince da cewa sabon Manajan Darakta kuma Shugaban hukumar, Alhaji Umar Abubakar Hashidu, shi ma ya kama aiki a matsayin riƙo kafin ya samu amincewar Majalisar Dattawa.

 

Dakta Gwarzo ya ce hakan ta faru ne bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban hukumar da sauran membobin a ranar 7 ga Mayu, 2023.

 

A cewar sa, Buhari ya kuma amince wa Lauya Bukar Baale da ya kama aiki a matsayin ciyaman mai riƙon ƙwarya na hukumar tare da membobi 10 na hukumar gudanarwar.

 

Bugu da ƙari, shugaban ya ba da umarni ga jami’in da ke riƙe da ofishin manajan daraktan hukumar a yanzu da miƙa ragamar ga sabon da aka naɗa ba tare da ɓata lokaci ba.

 

Gwarzo ya ce an ba da wannan umarnin ne domin “a kauce wa samun giɓi a wajen gudanar da ayyukan yau da kullum a wannan hukumar mai matuƙar muhimmanci da tasiri kafin lokacin da Majalisar Dattawa za ta ba su tabbacin naɗin su.”

 

Ita dai Hukumar Gudanarwar ta NEDC ta ƙunshi membobi kamar haka: Suwaiba Idris Baba, Babbar Daraktar Harkokin Agaji (daga Taraba, Arewa-maso-gabas); Musa Umar Yashi, Babban Daraktan Gudanarwa da Harkar Kuɗi (daga Bauchi, Arewa-maso-gabas); Dakta Isma’ila Nuhu Maksha, Babban Daraktan Gudanarwa (daga Adamawa, Arewa-maso-gabas), da Umar Abubakar Hashidu, Manajan Darakta/Shugaba (daga Gombe, Arewa-maso-gabas).

 

Sauran su ne Onyeka Gospel-Tony, Memba, (daga Kudu-maso-gabas); Hon. Madam Hailmary Ogolo Aipoh, Memba (daga Kudu-maso-kudu); Eya Kwamanda Babatunde Akanbi (ritaya), Memba (daga Kudu-maso-yamma); Mustapha Ahmed Ibrahim, Memba (daga Arewa-maso-yamma); Hadiza Maina, Memba (daga Arewa-ta-tsakiya), Alhaji Grema Ali, Memba (daga Arewa-maso-gabas), da kuma wakili daga Ma’aikatar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa ta Tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here