Kwana 6 kafin saukar Buhari NNPC ya ci gaba da hako mai a Borno

0
114

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya ci gaba da aikin hako danyen mai a yankin Tafkin Chadi da ke Jihar Borno, bayan shekara shida da dakatar da aikin.

An ci gaba da aikin ne washegarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da Matatar Mai ta Dangote, wadda ita ce mafi girma a Afirka, wadda ake sa ran za ta taimaka wajen rage wahalar mai a Najeriya.

Kamfanin NNPP na da kaso 20 cikin 100 na hannun jarin sabuwar matatar mai karfin samar da tataccen mai ganga 650,000 a kullum, mallakin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote.

Matata dai sa ran masana’antar da ta biya bukatun man Najeriya 100% har ta ba wa wasu kasashe 12 na Afirka, inda ake hasashen za ta rikar da kashi 36 na man da ake bukata a nahiyar.

Ana sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron kaddamar da dawowar aikin Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno, ta intanet a ranar Talata, kwana shida kafin saukarsa daga mulki.

A shekarar 2017 ne aka dakatar da aikin neman danyen mai a rijiyoyin man masu suna Wadi-1 da kuma Kinasar-1, da ke yankin Tuba, sakamakon harin da mayakan Boko Haram suka kai wa ma’aikatan da ke aikin a lokacin.

Sai dai daga bisani, bayan bincike da samun tabbacin tsaro, NNPC ta ci gaba da aikin a shekarar 2022 rijiyar mai ta Wadi-B.

Babban Daraktan NNPCL mai kula da Hako Mai, Mukhtar Zanna, ya ce kamfanin ke amfani da fasahar zamani, kuma yana da kwarin gwiwar samun danyen mai da iskar gas da dangoginsu a rijiyar.

Shi ma a nasa bangaren, Aminu Maitama, wanda shi ne babban daraktan ayyukan hakar mai na NNPCL, ya ce, “Mun yi amannar cewa yawan danyen man da za a samu a yankin zai isa kasuwanci.”

Aikin dai ya fara samo asali ne daga shekarar 1976, da aka fara binciken gano danyen mai, a yankunan Gubio da Maiduguri da kuma Baga, kafin a ci gaba da shi a 1996.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here