Inuwa Yahya ya zama sabon shugaban gwamnonin arewacin Najeriya

0
43

Gwamnonin arewacin Najeriya sun zabi Gwamnan Jihar Gombe Inuwa Yahya a matsayin sabon shugaban su domin maye gurbin Simon Lalong na Jihar Filato wanda ke kawo karshen wa’adin mulkin sa a makon gobe. 

Rahotanni sun ce daukacin gwamnonin yankin arewacin kasar 19 sun amince da zabin Inuwa ba tare da hamayya ba, a wani taron da suka gudanar a birnin Abuja.

Yayin jawabi bayan tabbatar masa da mukamin, sabon shugaban gwamnonin Inuwa Yahya ya sha alwashin gudanar da shugabanci na gari ba tare da nuna banbanci siyasa a tsakanin su ba.

Sabon shugaban yace zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin ci gaba da dorewar kungiyar domin taimakawa wajen samar da yanayin ci gaban al’ummar yankin da kuma samar musu da makoma mai kyau.

Gwamnan yace kamar yadda tsarin kungiyar ya tanada, zai dora daga inda shugabannin kungiyar da suka wuce suka tsaya, musamman abinda ya shafi bunkasa tattalin arziki da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Yahya yace matsalar tsaro a yankin arewa maso gabas da rikicin kabilanci da addini a yankin arewa ta tsakiya da kuma rikici tsakanin manoma da makiyaya a yakin arewa maso yamma suna daga cikin manyan kalubalen da suka addabi arewacin Najeriya ayau.

Sai dai yace duk da dabaibayin da wadannan matsaloli suka yiwa arewacin Najeriya, abinda ya kaiga haifar da matsalar tattalin arziki, kungiyar gwamnonin ta taka rawa wajen inganta rayuwar jama’ar arewacin kasar.

Gwamnan yace zai yi iya bakin kokarinsa a matsayinsa na shugaban kungiyar domin ganin an samar da yanayin ci gaba mai kyau, wanda zai bunkasa yankin domin fafatawa da takwarorin sa na kudancin kasar da kuma wasu yankunan kasashen duniya dan ganin mazaunansa sun samu shugabanci na gari.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Yahya ya kuma bayyana farin cikinsa da sake dawo da aikin neman mai a yankin Tafkin Chadi, abinda ya nuna cewar yanzu haka yankunan arewa guda 3 ke kokarin samar da man, wadanda suka hada da Kolmani a jihohin Gombe da Bauchi da kuma jihar Nasarawa baya ga na Tafkin Chadin.

Gwamnan ya jaddada cewar za suyi iya bakin kokarinsu wajen ganin wadannan ayyuka sun dore yadda jama’a zasu ci moriyar arzikin da Allah Ya wadata yankin da shi.

Yahya ya kuma kara da cewar yankin arewacin Najeriya na kuma dauke da wasu tarin arzikin ma’adinai da ya dace a mayar da hankali akansu bayan na mai da iskar gas.

A karshe Yahya ya jinjinawa Gwamna Simon Lalong saboda irin jagorancin da ya samar, yayin da yace zai ci gaba da aiki da tsoffin shugabannin da suka jagoranci kungiyar gwamnonin domin samun nasara. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here