An gurfanar da malamin da ya yi wa dalibarsa fyade a Legas

0
90

An gurfanar da wani malami mai shekaru 35 a Legas, Olayiwola Ololade, a gaban wata kotun majistare, Yaba, bisa zargin yi wa wata daliba ‘yar shekara 15 fyade a harabar makarantar da ke unguwar Mushin.

Lauyan mai shigar da kara, Thomas Nurudeen, ya shaida wa kotun cewa, wanda ake kara a ko da yaushe ya kan nemi dalibar da ya gan shi a ofishinsa bayan kammala karatu, sannan ya yi lalata da ita, inda ya yi mata barazanar cewa zai tabbatar da cewa an kore ta daga makarantar idan ta yi kokarin tona masa asiri.

Ya ce daga baya wadda abun ya shafa ta fallasa lamarin, inda ta ba da labarin abin da malamin ke yi mata.

Alkalin kotun, Mista P E Nwaka, ya bayar da umarnin tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali har zuwa lokacin da daraktan shigar da kara na kasa (DPP) zai ba da shawara a kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here