Alba zai bar Barca kafin kwantaraginsa ya kare

0
79

Barcelona da Jordi Alba sun cimma yarjejeniyar raba gari tun kan kwantiraginsa ya kare a kungiyar.

Alba, mai shekara 34 ya koma Camp Nou a 2012 daga Valencia, ya kuma lashe La Liga shida da Copa del Rey biyar da Champions League a 2015.

Ya buga wa Barcelona wasanni 458 har da 29 a kakar nan da kungiyar Camp Nou ta dauki La Liga na bana na 27 jimilla.

Alba ya zama na biyu da zai bar Barcelona a karshen kakar nan, bayan kyaftin, Sergio Busquets.

Barcelona ta kai ga cimma wannan matsaya, bayan da take son cika ka’idar La Liga ta kashe kudi daidai samu, wato financial fair play.

Barcelona ta sayar da Lionel Messi bayan da ta fada matsin tattalin arziki, wadda daga baya ta nemi kudin sayo wasu ‘yan kwallon har da Jules Kounde daga Sevilla.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here