Dokokin da Buhari ya sanya wa hannu kafin barin mulki

0
106

Baya ga kaddamar da wasu jerin ayyuka har 14 da Shugaba Buhari yake yi a daidai lokacin da yake bankwana da mulkin Nijeriya, Buhari ya kuma sanya hannu kan wasu dokoki, wadanda Majalisun Dokokin Tarayya suka mika masa don amincewa da su.

Mai taimaka wa shugaban kan harkokin sada zumunta na zamani Bashir Ahmad ne ya zayyana jerin dokokin takwas a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

Sai dai duk da wadannan dokoki takwas da Buhari ya sanya wa hannu kwana shida kafin ya bar mulki, ga alama akwai wasu da ba lallai shugaban ya kai ga sanya hannu a kansu ba cikin sauran kwanakin da suka rage masa.

Ahmad ya ce har yanzu akwai wasu karin dokokin a gaban shugaban kasa bai sanya hannu a kansu ba. Saboda yana tantancewa da zabo wadanda za su amfani talakan Nijeriya.”

Ga dai jerin dokoki takwas da abin da suke nufi:

  • Dokar Shirin Zuba Jari Kan Dan Adam ta Kasa (National Social Investment Programme Agency Act)

An samar da wannan doka ce don taimakawa wajen karfafa rayuwar talaka da agaza masa a Nijeriya.

Dokar za ta samar da tsari da yanayin dokokin da za su bayar da damar a kafa Hukumar Gina Rayuwar Mutanen Nijeriya.

Dokar Hukumar Kula da Makarantun Sakandire ta Kasa (National Senior Secondary Education Act.).

  • Dokar Hukumar Kula da Makarantun Sakandire ta Kasa za ta kafa hukuma, sannan ta kayyade dokokin da matakan da ya kamata ilimin sakandire ya taka a kasar.

Za kuma ta samar da yanayin da za a dinga kula da ilimin sakandire a Nijeriya.

  • Dokar Nazarin Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Ila-Orangun (Federal University of Health Sciences Ila-Orangun (Establishment) Act).

Wannan doka ta bayar da damar a kafa sabuwar Jami’ar Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Tarayya a garin Ila-Orangun da ke jihar Osun a kudu maso-yammacin Nijeriya.

  • Dokar kafa Jami’ar Nazarin Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Ila-Orangun (Federal University of Health Sciences Ila-Orangun (Establishment) Act).

Ita ma wannan doka ta bayar da damar a kafa sabuwar Jami’ar Nazarin Kimiyyar Lafiya ta Tarayya a garin Azare da ke jihar Bauchi a arewa maso-gabashin Nijeriya.

Wadannan jami’o’i za su samar da dalibai kwararru a fannin kiwon lafiya wanda har yau a Nijeriya yake fuskantar karancin kwararrun ma’aikata da kayan aiki.

Haka zalika za su zama damar samar da guraban ayyukan yi ga ‘yan kasar.

  • Dokar kafa Cibiyar Nazarin Ayyukan Cigaba da Gudanarwa (Chartered Institute of Development Studies and Administration of Nigeria (Establishment) Act)

Wannan doka za ta bayar da sarari na kafa wata cibiya wadda za a dinga nazarin hanyoyin kawo cigaba ga kasa da al’umma.

Jami’an da ke tsara manufofin ci gaban al’umma ne za su dinga samun horo don kwarewa a wannan cibiya.

Cibiyar Horar da Injiniyoyi da tantance su (The Chartered Institute of Power Engineers of Nigeria Act)

  • Dokar Cibiyar Horar da Injiniyoyi da Tantance su za ta bayar da damar a samar da Cibiyar Horar da Injiniyoyi da Tantance su.

Wannan cibiya na da alhakin bayyana matakin ilimi da kwarewar da ake bukatar Injiniya ya samu kafin a kira shi da wannan siffa.

  • Dokar kafa Cibiyar Binciken Masana’antu ta Tarayya (Federal Institute of Industrial Research (Establishment) Act).

Wannan doka za ta jagoranta tare da bayar da dama ga gwamnatin Nijeriya ta samar da wata cibiya da za a dinga gudanar da bincike kan masana’antu da yadda suke gudanar da ayyukansu a kasar.

  • Dokar kafa Cibiyar Nazarin Dabarun Gudanarwa ta Nijeriya (Institute of Strategic Management of Nigeria Act.).

Doka ce da za ta bayar da tsari da yanayin da gwamnati za ta kafa wata cibiya da masu ayyukan gudanarwa a kasar za su dinga samun horo don inganta aiyukansu.

Cibiyar na da manufar ganin ayyukan gudanarwa a dukkan matakan gwamnati sun kyautatu.

Yawan dokokin da aka gabatar

TRT Afirka ta ruwaito cewar, a wani taro da majalisar dattawa mai barin gado karkashin jagorancin Sanata Ahmad Lawal ta shirya wa sabbin ‘yan majalisa masu shigowa a Abuja a ranar 9 ga Mayu, an jiyo Ahmad Lawal na cewa ya zuwa watan Yulin 2022, majalisar ta aike wa Shugaba Buhari kudirin doka 162, inda shugaban ya rattaba hannu da amincewa kan 104 daga ciki.

Lawal ya kara da cewa wannan ne adadi mafi yawa na dokoki da aka amince da su tun bayan dawowar dimokuradiyya a 1999.

Ya ce an samu wannan nasara ne sakamakon fahimtar juna tsakanin majalisa da bangaren zartarwa.

Bashir Ahmad ya ce Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne mai kyakkyawar alaka da sauran bangarorin gwamnati, kuma yana bai wa kowa damar aikinsa, ba ya karfa-karfa ko katsalandan.

“Ya sanya hannu kan dokoki da dama, kuma yana yin hakan ne bayan nazari kan kowacce doka da majalisar kasa ta gabatar masa.”

Akwai wasu dokokin da Shugaba Buhari zai sanya hannu a kai a ‘yan kwanakin da suka rage masa?

Duba da yadda Sanata Lawal ya ce an kai wa Shugaba Buhari dokoki sama da 160 kuma ya amince da 104 ne, ko hakan na nufin akwai wasu dokokin da shugaban ya ki sanyawa hannu?

Bashir Ahmad ya ce wa TRT Afrika “Akwai wasu dokoki a gaban shugaban kasa da har yanzu bai sanya hannu a kansu ba. Saboda yana tantancewa da zabo wadanda za su amfani talakan Nijeriya.”

Da aka tambaye shi ko sabbin dokokin da aka sanya hannu a kai za su bar nauyi babba kan gwamnati mai zuwa?

Bashir ya amsa da cewa “Ai gwamnati cigaba ce kan wasu ayyukan na baya, gwamnatin jam’iyyarmu ce, kuma ana sa ran za ta dora kan ayyukan alherin da ta samu na wannan gwamnati.

Ya kara da cewa, Bola Tinubu da zai karbi mulki wani bangare ne na mulkin Buhari na shekara takwas, kuma Buharin zai mika masa kundin yadda ya gudanar da mulki na tsawon wadannan shekaru.

“Sabbin dokokin duk sun shafi rayuwar talakan Nijeriya”

Mataimakin na Shugaba Buhari kan soshiyal midiya ya kuma kara da cewa idan aka kalli dukkan dokokin, “za a ga sun shafi rayuwar talaka ne baki daya.”

Ya ce babu daya daga ciki da za ta amfani wani mutum shi kadai, dukkan ‘yan kasa ne za su amfana da wadannan kudurorin doka da Shugaba Buhari ya sanya wa hannu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here