Van Nistelrooy ya bar PSV Eindhoven tun kafin gama kakar bana

0
97

Ruud van Nistelrooy ya bar PSV Eindhoven tun kafin a kammala kakar bana, saboda rashin samun goyon bayan kungiyar in ji wata sanarwa.

Van Nistelrooy ya lashe kofin kalubale na Holland wato Dutch Cup da na zakaru na kasar wato Dutch Super Cup tun bayan da ya karbi ragamar kungiyar a Maris din 2022.

PSV ta sanar da cewa ta tsara tattaunawa da shi ranar Lahadi kan batun tsawaita zamansa a kungiyar, amma mai shekara 46 ya ajiye aikin.

Kungiyar da take ta biyu a teburin Eredivisie ta ce ta ji takaici da wannan matakin da kocin ya dauka.

PSV ce ta daya da tazarar maki 10 tsakaninta da Feyenoord, wadda ita kuma ta bai wa Ajax ta ukun teburi tazarar maki uku.

Kungiyar za ta yi kokarin ganin ba a doke ta ba a gidan AZ Alkmaar a karshen mako, domin ta samu matakin gurbin shiga Champions League.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here